ABNA24 : Sakamakon da wasu manyan gidajen talabijin na Isra’ilan suka fitar da daren jiya Talata suna nuni da cewa Netanyahu tare da jam’iyyu masu goya masa baya sun gaza wajen rinjaye a majalisa, lamarin da a ke ganin za’a fuskanci makonni na rashin tabbas ko kuma ma a sake gudanar da wani zaɓen a karo na biyar.
Idan dai har sakamakon ya ci gaba kamar yadda ake kirdado, ko kuwa Netanyahun da masu adawa da shi suna buƙatar haɗā gwuiwa da tsohon ministan tsaro kana kuma tsohon abokin Netanyahun wajen samun rinjaye na alal aƙalla kujeru 61 a majalisar Knesset mai kujeru 120.
Netanyahun dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba da yahudawan na ya sauka daga karagar mulki sakamakon zarginsa da ake yi da rashawa da cin hanci da kuma almundahana da dukiyar gwamnati.
342/